Gwamnonin APC Sun Bukaci DSS Ta Kamo Masu Son Kafa Gwamnatin Riko a Nijeriya

Gwamnonin  APC Sun Bukaci DSS Ta Kamo Masu Son Kafa Gwamnatin Riko a Nijeriya

Gwamnonin jam'iyyar All Progressives Congress (APC), sun buƙaci rundunar tsaron farin kaya (DSS) da ta cafke sannan ta tuhumi waɗanda ke shirin kafa gwamnatin wucin gadi a ƙasar nan.

 Rahoton The Cable A ranar rundunar tsaron farin kayan ta bayyana cewanta bankafo shirin wasu mutane na kafa gwamnatin wucin gadi domin hana rantsar da Bola Tinubu a matsayin shugaban ƙasa. Rahoton Arise News 
"Bayan an fafata a zaɓe, jam'iyyu suna da ƴancin zuwa kotu domin neman haƙƙin su." A cewar Bagudu. 
 “Tabbas, kowa yasan cewa jam'iyyun PDP da LP sun zaɓi da suje gaban kotun sauraron ƙararrakin zaɓen shugaban ƙasa domin ƙalubalantar sakamakon zaɓen shugaban ƙasa wanda Asiwaju Bola Ahmed Tinubu APC ya lashe. 
“A dukkanin jihohin ƙasar nan an kafa kotuna domin bayar da dama ga waɗanda suka yi takara a zaɓen kuma basu gamsu ba, su ƙalubalanci sakamakon." 
"Muna kira ga ƴan Najeriya da su mayar da hankali sannan su yi baya da duk wani irin abu da ka iya kawo naƙasu ga dimokuraɗiyyar mu." 
“Ƙasar mu tayi ƙoƙari sosai wajen tallata dimokuraɗiyya a cikin gida da ƙasashen Afrika, sannan akwai takaici ace wasu marasa kishin ƙasa suna ƙulla shirin kafa gwamnatin wucin gadi wacce zata rusa dimokuraɗiyyar mu."