Gwamnatin Tarayya Ta Soke Dakatarwa Kan Tweeter

Gwamnatin Tarayya Ta Soke Dakatarwa Kan Tweeter
Gwamnatin tarayya ta ɗage dakatarwa da ta yi wa kafar sadarwa ta Tweeter a Nijeriya bayan samun amincewar shugaba Buhari.
Wannan matakin shugaban kwamitin sadarwa kuma shugaban hukumar sadarwa ta Kashifu Inuwa Abdullahi, ne ya sanar da hakan.
Kashifu, a bayanin da ya fitar a Abuja ya ce amincewar ta shugaban ƙasa ta biyo bayan takardar neman amincewa da ministan sadarwa na ƙasa Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami
Gwamnatin Nijeriya ta dakatar da kafar ne kusan shekara ɗaƴa sai yanzu ne gwamnati ta janye dakatarwar.