Gwamnatin Tarayya Ta Baiwa Jihar Sakkwato Tallafin Biliyan 9 Don Taimakawa Jama'a

A tsarin rabon kudin Sakkwato ce jiha ta hudu a cikin wadan da suka fi samun kudin masu yawa. Nasarawa, Cross River, Zamfara, Sai Sakkwato in da ta samu Biliyan 9,193,398141.98

Gwamnatin Tarayya Ta Baiwa Jihar Sakkwato Tallafin Biliyan 9 Don Taimakawa Jama'a

Gwamnatin Tarayya a karo na biyu ta rabawa jihohi da Abuja makudan biliyoyin kudi don samar da sauki ga al'umma.
Sanarwar ta ce Biliyan 135 da Miliyan 479 da dubu 884 da 677 jihohi da Abuja za su raba karkashin shirin NG-CARES  a kokarin da ake yi na dawo da hayacin tattalin arziki bayan cutar COVID-19.
Bankin duniya ke tallafawa shirin don farfado da tattalin arziki wurin taimakon talaka da mabukaci da magidanta da karamin manomi da karami da matsakaicin Dan kasuwa, da cutar korona ta shafa.
A tsarin rabon kudin Sakkwato ce jiha ta hudu a cikin wadan da suka fi samun kudin masu yawa.
Nasarawa, Cross River, Zamfara, Sai Sakkwato in da ta samu Biliyan 9,193,398141.98
Ministan Kasafi da tattalin arziki a takardar da ya fitar ya godewa bankin duniya tare da kira ga Gwamnoni su mayar da hankali wurin yakar bakin talaucin da ya addabi mutane.
An kasafta kudin ne gwargwadon yadda jihohi suka kula da yakar cutar Korona a lokacin da ta shigo, tsari da daukar mataki na jihohi aka duba a wancan lokaci aka raba kudin.
Sanda aka yi cutar jihar Sakkwato ita ce ta hudu a Nijeriya wajen daukar matakin Korona hakan ya sa aka samu wadan nan makudan kudi da za a yi amfani da su yanda yakamata lalle Sakkwato za ta dawo cikin hayacinta.
Yakamata a godewa tsohuwar Gwamnatin Sanata Aminu Waziri  Tambuwal a wannan nasarar da aka samu domin kokarinta ne ya Kawo wannan arzikin.