Gwamnatin Tarayya ta ayyana ranar hutun Kirsimeti da Sabuwar Shekara
Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida ta Tarayya ta ayyana ranakun 25 da 26 ga Disamba, 2024, da kuma 1 ga Janairu, 2025, a matsayin ranakun hutu na jama’a don bikin Kirsimeti, Ranar Kyauta (Boxing Day), da kuma Sabuwar Shekara.
Wannan sanarwa ta fito ne daga wata takarda Da babban Sakatare na ma’aikatar, Dokta Magdalene Ajani, ta sanya wa hannu.
Ministan Harkokin Cikin Gida, Dokta Olubunmi Tunji-Ojo, a madadin Gwamnatin Tarayya, ya yi kira ga ‘yan Najeriya da mazauna kasar su yi amfani da wannan lokaci na bukukuwa don tunawa da darajar soyayya, zaman lafiya, da hadin kai da ake son lokaci irin wanan.
Channels Television ta rawaito cewa Dokta Tunji-Ojo ya jaddada muhimmancin wannan lokaci na bukukuwan, yana mai cewa yana da matukar amfani wajen karfafa zumunci da dangantaka tsakanin iyalai da al’ummomi.
managarciya