Gwamnatin Tarayya ta Ayyana Ranar 11 da 12 ga Watan Yuli A Matsayin Ranar Hutun Sallah

Gwamnatin Tarayya ta Ayyana Ranar 11 da 12 ga Watan Yuli A Matsayin Ranar Hutun Sallah

 

Daga Jabir Ridwan.

 

Gwamnatin tarayya ta ayyana ranar litinin 11 da talata 12 ga Watan Yuli da muke ciki a matsayin ranar hutu domin gudanar da bukin sallar layya (Eid Kabir).

 
Wannan dai na kunshe ne acikin wani bayani da  ministan lamurran cikin gida Rauf Aregbesola ya fitar Mai sa hannun babban sakataren maaikatar Dr shu'aibu Belgore a ranar Alhamis.
 
Ministan hakama yayi amfani da damar wajen Taya daukacin al'ummar musulmin kasar nan murnar dama wadanda ke zaune kasashen ketare.
 
An ruwaito ministan na cewa " Ina kira ga ga al'umma musulmi da su so juna tareda zaunawa lafiya kazalika da kyautatawa Yan uwa, hakama ministan yaja hankalin su da suyi amfani da wannan lokaci wajen yiwa kasar nan addu'a domin samun zaman lafiya Mai dorewa  duba da irin qalubalen da kasar ke ciki na matsalar tsaro".
 
Ministan  ya bayarda tabbacin cewa gwamnatin shugaba buhari bazatayi kasa a guiwa ba wajen kare rayukan Yan kasa, Samar musu da walwala da Jin dadi tareda Kara inganta tsaro a daukacin makarantun kasar nan.
 
Aregbesola ya shawarci al'ummar musulmin kasar nan da su Kai rahoton duk wani Abu da Basu gamsu dashi ba wajen jami'an tsaro Mafi kusa dasu ta hanyar amfani da sabuwar na'urar (N alert) wadda aka assasa da zummar isarda Sako cikin gaggawa ga jami'an tsaro musamman a wannan lokaci da ake fuskantar matsala tsaro.
 
Jaridar Intelregion ta ruwaito ministan na cewa lamarin tsaro ba aikin mutum guda bane, akwai bukatar hada Karfi da karfe wajen shawo kan matsalar.
 
A karshe ministan ya bayarda tabbacin cewa gudumuwa da hadin Kai daga Yan kasar nan musamman a wannan lokaci na bukin sallar layya zai taimaka gaya wajen baiwa jami'an tsaro damar kare rayukan al'umma.