Gwamnatin tarayya ta amince da kashe Naira Biliyan 700 don gyara filin jirgin sama na Legas ya yin da na Kano aka ware masa Biliyan 46

Majalisar Zartarwa ta Tarayya (FEC) ta amince da kwangiloli da suka haura Naira biliyan 900 domin sabunta ababen more rayuwa a fannin sufurin jiragen sama a faɗin ƙasa.

Ministan Sufurin Jiragen Sama, Festus Keyamo, ya bayyana cewa an ware Naira biliyan 712 domin gyaran terminal ɗaya da faɗaɗa terminal biyu na Filin Jirgin Sama na Murtala Muhammed da ke Legas, ciki har da sabbin fitilu, hanyoyin shiga da wuraren ajiye jirage.

An kuma amince da gyaran Filin Jirgin Sama na Malam Aminu Kano da na Fatakwal, da sabunta fitilun tashi da saukar jirage zuwa matakin zamani na CAT 2.

FEC ta amince da gina sabuwar katangar tsaro da ke da tsawon kilomita 14.6 a filin jirgin Legas, tare da na’urorin gano kutsen tsaro da hasken rana, wanda zai ci Naira biliyan 49.89.

Haka kuma, an amince da hayar Filin Jirgin Sama na Akanu Ibiam da ke Enugu na tsawon shekaru 30 ga kamfanin mai zaman kansa, domin rage asarar da ake samu daga filayen jirage ƙanana.

Keyamo ya ce wannan mataki zai taimaka wajen samar da riba daga sassan da ba su shafi jirage kai tsaye ba kamar cibiyoyin kasuwanci da taruka.