Home Rahoto Gwamnatin tarayya ta amince da karin albashi kashi 40 ga malaman jami’a

Gwamnatin tarayya ta amince da karin albashi kashi 40 ga malaman jami’a

4
0

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta amince da ƙarin albashi kashi 40 cikin 100 ga malaman jami’o’in tarayya, bayan fiye da shekaru 16 na tattaunawa da yajin aiki tsakaninta da ƙungiyar malaman jami’o’i (ASUU).

Ministan ilimi, Dakta Tunji Alausa, ya bayyana hakan a Abuja yayin ƙaddamar da sabuwar yarjejeniyar da aka cimma tsakanin gwamnati da ASUU, wadda za ta fara aiki daga 1 ga Janairu, 2026.

Ya ce yarjejeniyar ta ƙunshi ingantaccen tsarin fansho, yadda farfesoshi za su yi ritaya a shekara 70 tare da fansho da ya yi daidai da albashinsu na ƙarshe, da kuma ƙaddamar da Consolidated Academic Tools Allowance domin tallafa wa bincike da koyarwa.

Yarjejeniyar ta kuma tanadi sabon tsarin tallafi ga jami’o’i, ciki har da kuɗaɗen bincike da kafa hukumar bincike ta ƙasa da za a rika ware mata aƙalla kashi 1 na tattalin arziki.

Shugaban ASUU, Farfesa Chris Piwuna, ya bayyana yarjejeniyar a matsayin babbar nasara, sai dai ya ce har yanzu akwai batutuwan ikon jami’o’i da ke bukatar kulawa.

Masana da ɗalibai sun yaba da matakin, suna kira da a aiwatar da yarjejeniyar gaba ɗaya domin ta amfani ɓangaren ilimi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here