Gwamnatin Taraiya ba za ta iya hana jihohi da ƙanan hukumomi su yi amfani da asusun haɗaka ba
Gwamna Ahmadu Fintiri na Adamawa ya ce Gwamnatin Tarayya da Majalisar Tarayya ba za su iya iyakance yadda gwamnatocin Jihohi da Kananan Hukumomi za su rika kashe kason su na gwamnatin taraiya ba.
Fintiri ya bayyana haka ne a wata hira da gidan Talabijin na Channels TV, shirin Hard Copy, wanda aka gabatar a jiya Juma’a.
A cewarsa, dukkan gwamnoni sun yi na’am da hukuncin da kotun koli ta yanke, wanda ya bai wa kananan hukumomin ‘yancin cin gashin kai.
Sai dai ya ci gaba da cewa, babu wani laifi idan gwamnatocin jihohi da na kananan hukumomi sun amince su yi amfani da asusun hadaka na ayyukan hadin gwiwa.
Ya ce: “Wa ya ke ba Gwamnatin Tarayya umarnin yadda za ta kashe kudaden ta? Wa ya ke ba Majalisar Dokoki ta Kasa umarnin yadda za su kashe kudin da ake basu?
"Idan karamar hukumar ta yanke shawarar cewa za ta yi hadin gwiwa don yin aiki tare kuma sun yi kasafin kudin akan hakan, kuma suka kuɗin a asusun haɗaka, me ye matsalar hakan?"
managarciya