Gwamnatin Sokoto ta kaddamar da rabon Keke Napep da Babura 1500

Gwamnan ya kadamar ababen hawan tun a shekarar data gabata ta 2024 amma ba a raba kayan sai a wannan shekara, mutane da dama sun baiwa gwamnati shawara ta daina irin wannan halin tarika raba kaya a duk sanda ta kaddamar da su.

Gwamnatin Sokoto ta kaddamar da rabon Keke Napep da Babura 1500
 
Gwamnatin jihar Sokoto ta raba babura 1,000 da keke Napep guda 500 ga ƴan Achaɓa bisa farashi mai rahusa. 

Gwamnatin ƙarƙashin jagorancin Gwamna Ahmed Aliyu ta raba ababen hawan ne akan rangwamen kaso 80% cikin kaso 100%
Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa Gwamna Ahmed Aliyu, ya ƙaddamar da rabon ababen hawan a ranar Asabar, 4 ga watan Janairun 2024. 
Gwamna Ahmed Aliyu ya ce an yi hakan ne domin sauƙaƙa zirga-zirga a cikin manyan biranen jihar da ƙananan hukumomin jihar ga talakawa. 
Ya ƙara da cewa hakan na daga cikin matakai da dama da aka ɗauka na samar da ƙarin ayyukan yi a jihar, tare da kyautata rayuwar waɗanda suka amfana da iyalansu. 
A cewarsa, an sayi keke Napep ɗin kan kudi N3.6m, sannan kuma an sayi baburan kan N1.3m, amma an raba su a kan farashi mai rahusa. 
"Muna ba da keke Napep a kan N1m da babur a kan N300,000 bayan an biya kuɗin farko na N150,000 na keke Napep da N50,000 na babur tare da mutum ɗaya da zai tsayawa kowane mai cin gajiyar shirin."
"Ana sa ran waɗanda suka ci gajiyar shirin za su rika biyan N15,000 (na keke Napep) da kuma N5000 (na babur) a kowane wata."  
Gwamna Ahmed Aliyu A yayin da ya buƙaci waɗanda suka ci gajiyar tallafin da su rangwantawa fasinjojinsu ta hanyar rage farashi, ya gargaɗe su da karya ƙa’idojin yarjejeniyar.