Gwamnatin Sokoto ta fara biyan mafi ƙarancin albashi a wannan watan

Gwamnatin Sokoto ta fara biyan mafi ƙarancin albashi a wannan watan
Gwamna Ahmed Aliyu na jihar Sokoto ya amince da fara biyan sabon mafi karancin albashi na Naira dubu 70 ga ma'aikatan jihar.
Sanarwar da gwamnati ta fitar ta ce ma’aikatan gwamnati za su samu sabon mafi karancin albashin da zai fara daga albashin su na watan Janairu da mu ke ciki.
Sanarwar mai dauke da sa hannun Mista Abubakar Bawa, Babban Sakataren Yada Labarai na Gwamnan ya ce biyan kudin zai shafi ma’aikatan gwamnati da ma’aikatan kananan hukumomi a fadin jihar.
Ya ce biyan sabon mafi ƙarancin albashin wani cika alkawari ne da gwamnan jihar ya ɗauka tun a baya.