Gwamnatin Sokoto Ta Dauki Nauyin Karatun Dalibai 15 a Kasar China

Gwamnatin Sokoto Ta Dauki Nauyin Karatun Dalibai 15 a Kasar China

Gwamnatin Sokoto Ta Dauki Nauyin Karatun Dalibai 15 a Kasar China


Gwamnatin jihar Sakkwato za ta tura ɗalibai 'yan asalin jihar zuwa ƙasar China domin su yi karatu, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito. 
Gwamnatin ƙarƙashin jagorancin Gwamna Ahmed Aliyu ta ɗauki nauyin karatun daliban su 15 zuwa ƙasar China kuma za su tafi nan ba da jimawa ba. 
Shugaban hukumar bayar da tallafin karatu ta jihar Sokoto, Abdulkadir Dan’iya ne ya bayyana hakan a wata hira da manema labarai a ofishinsa ranar Juma’a. 
Ya kuma yi bayanin cewa ɗaliban da za su ci gajiyar wannan tallafin karatu, za su karanci kwasa-kwasan injiniyarin daban-daban a ƙasar Sin. 
Abudulƙadir Ɗan'iya ya kuma bayyana cewa zasu bar ƙasar nan a makon farko ko kuma mako na biyu na watan Nuwamba mai zuwa a 2023 da muke ciki. 
 
Shugaban hukumar bada tallafin karatun ya ce: "A halin yanzu suna kan ɗaukar horo da kuma wayar da kai wanda ya zama wajibi saboda zaman da zasu yi a ƙasar waje." 
"Tuni gwamnatin jihar Sakkwato ta biya masu kuɗin makaranta da sauran hidindimun da zasu yi yayin zaman karatu a can ƙasar." 
Dan’iya ya kara da cewa za a kara daukar nauyin karatun wasu dalibai a kasashen waje domin su karanci kwasa-kwasan da suka dace da jama’a.