Gwamnatin Najeriya ta umurci  bankuna su kara kudin da suke cirewa idan mutum ya ciri kudi a ATM

Gwamnatin Najeriya ta umurci  bankuna su kara kudin da suke cirewa idan mutum ya ciri kudi a ATM

Daga ranar 1 ga watan Maris wato farkon Azumi, duk wanda ya ciri dubu 20,000 a cikin ATM din da ba na bankinsa ba za a zare masa N100 a matsayin kudin harjin aiki da ATM, haka za a rika zarar N100 a duk Naira dubu 20,000 da ya cire.

Sannan duk wanda ya yi amfani da ATM din bankin da ba nashi ba a wuraren da ba harabar banki ba, alal misali a gidajen Mai ko Kantin sayar da kaya da sauransu za a caje shi N100 sannan da kuma karin N500 a duk Naira dubu 20,000 da zai cira (sai idan mutum ya je cire kudin zai ga asalin nawa za a caje shi)

A yanzu dai ana cazar N35 ne a duk cire kudi sau Uku a bankin da ba na mutum ba. Amma a wata sanarwa da Babban Bankin Najeriya CBN  ya fitar sanarwar ta ce "saboda yadda abubuwa suka yi tsada yasa dole bankunan suka yi kari kan kudin zuwa N100 da kuma N500"
Me zaku ce?