Gwamnatin Najeriya Ta Gargadi 'Yan Siyasa Kan Amfani Da 'Yan Bangar Siyasa

Gwamnatin Najeriya Ta Gargadi 'Yan Siyasa Kan Amfani Da 'Yan Bangar Siyasa
 
Daga Abbakar Aleeyu Anache 
 
Gwamnatin Najeriya ta gargadi Gwamnonin jihohin kasar 26 da su kaucewa yin amfani da yan bangar siyasa wajen hana abokan hamayyarsu gudanar da tarurrukan yankin neman zabe musamman ganin lokacin zaben shekara mai zuwa na karatowa, 
 
Mai baiwa shugaban kasa Muhammadu Buhari shawara akan harkokin tsaro Manjo Janar Babagana Monguno ya gabatar da wannan gargadi inda yake cewa an baza jami'an tsaro a fadin kasar domin murkushe duk wani yunkurin haifar da tashin hankali wajen zaben mai zuwa, 
 
Monguno yace abin takaici ne yadda Gwamnonin ke amfani da karfin mulki wajen tirsasawa abokan adawarsu maimakon gabatar da ayyukan da suka yi domin janyo hankalin masu kada kuri'u su zabi wadanda suke marawa baya,
 
Rahotanni sun ce jam'iyyun adawa na cigaba da fuskantar matsaloli sosai wajen tallata yan takararsu ta hanyar manna fastoci ko ta kafofin yada labarai ko kuma gudanar da tarurrukan yankin neman zabe, 
 
A makwannin baya ne kwamitin wanzar da zaman lafiya dake karkashin jagorancin tsohon shugaban kasa Janar Abddulsalam Abubakar ya jagoranci jam'iyyun siyasar da kuma yan takarar sun a shugaban kasa wajen rattaba hannu akan yarjejeniyar kaucewa tashin hankali lokacin yankin zaben da kuma yayin gudanar da zaben, 
 
Har ila yau an gudanar da irin wadannan bukukuwan rattaba hannu a matakan jihohi domin tabbatar da cewar shugabanin siyasar da yan takara sun mutunta dokar kaucewa tashin hankalin ko tinzira magoya bayansu haifar da rigima, 
 
Sai dai rahotanni dake fitowa daga wasu jihohi na nuna yadda ake kaucewa yarjejeniyar wajen musgunawa jam'iyyun dake adawa da gwamnatin dake ci a matakan jihohin,