Gwamnatin Kebbi ta rabawa manoma injin ban ruwa masu aiki da hasken rana guda 10,000
Gwamnatin jihar Kebbi karkashin Gwamna Dakta Nasir Idris ta rabawa manoma injin na ban ruwa masu aiki da haske rana waton sola har guda dubu 10 domin saukake masu harkokin noma a jihar.
Gwamna Dakta Nasir ya sanar da hakan ne a lokacin da yake ba da sanarwa zuwan minista mai kula da ma’aikatar noma ta Nijeriya da zai zo jihar a ranar Alhamis ta wannan satin domin kaddamar da bayar da tallafin da gwamnati ta samar.
Gwamnan ya ce ministan noma zai kaddamar da injin na ban ruwa na Sola 10,000 da za a baiwa manoma a fadin jihar Kebbi gaba daya.
Gwamna a lokacin da yake sanar da wannan cigaban ya ce gwamnatinsa za ta cigaba da samar da tallafi ga abubuwan da za su sanya harkar noma ta yi sauki ga manoma, an samar da wadan nan injin na Sola ne ganin yadda man fetur ya yi tsada, kuma yana son jihar Kebbi ta cigaba da rike kambinta a matsayin ta kan gaba wurin samar da shinkafa a Nijeriya.
Mai baiwa Gwamna shawara kan harkokin yada labarai Yahaya Sarki ne ya fitar da bayanin zuwan minista domin manoma su kwana da shirin aikin alherin da za su amfana da shi a wannan satin.
managarciya