Gwamnatin Jihar Kebbi ta yi zazzafan martani ga fitaccen malamin nan Imam Bashiru Muhammad Jega bayan wata ragargaza da ya yi wa Gwamnatin.
Arewa Updates ta rawaito cewa, a wani bidiyonsa mai mintuna 7 da sakan 5 da ya karaɗe kafafen sada zumunta malamin ya yi kaca-kaca da Gwamnatin jihar Kebbin.
Ya ce, yana kiran malamai su ji tsoron Allah su riƙa faɗar gaskiya, ya koka kan maganar da ya ce Sakataren Izala na Kasa Malam Kabiru Gombe ya yi na cewa duk Najeriya Gwamnan Kebbi na sawun gaba wajen Gwamnoni masu taimakon addini saboda ya je wata islamiyya da aka yi gobara cikin dare ya tsaya awa 2, tare da yin adduʼoʼi ga waɗanda ba sa son Gwamnan.
Malam Kabiru Gombe ya ce a faɗa masa wane Gwamna ne zai iya yin irin wannan?
Imam Bashir ya jefawa sakataren tambaya cewa, don Allah ya fadi Islamiyya nawa Gwamnan Kebbin ya gina?, ya ce Gwamnatin Kebbi ta samu kuɗaɗe masu yawa amma ina ayyukan da ta yi?
Ya ce, limamai a jihar Naira 4,000 ake basu ladanai kuma 2,000 duk wata, amma bai sani ba in an canja daga nan sai a faɗa masa, kuma haka ake bayar wa duk wata, ya ce, yanzu ina taimakon addini a nan?
Malamin ya ce, a maʼaikata wanda ake bai wa fansho 40,000 a Zamfara a Kebbi 4,000 ake ba shi.
Game da ƴan matan Maga ya ƙalubalancin Sakataren Izala ya sake bincike, ba wai kawai don ana baka abu ko ƙungiyarka sai ka fito ka yabe su.
Ya kuma bada misali da dakatar da Malam Abubakar Salihu Alƙali Zaria, inda ya ce daman ƙungiyoyi ba sa son a riƙa faɗar gaskiya.
Imam Bashiru ya ce, yana fatan Malam Kabiru Gombe ya yi masa raddi da kansa a nan ne zai ga asalin raddi.
Malamin ya ci gaba da cewa, maganar gidan yari ba barazana ba ce domin Sheikh Ibn Taimiyya ma an kai shi gidan yari.
A ƙarshe ya yi tsokaci kan kama Abubakar Malami inda ya bayyana shi da siyasa da yaƙi da adawa kawai, yana mai cewa in ba a son adawa da sai a bar wa sarakuna su yi ta mulki kawai.
To sai dai da alama wannan kalamai sun fusata Gwamnatin Jihar Kebbin inda ta mayar da martani mai zafi.
Mai ba wa Gwamnan Jihar Kebbi shawara kan Addinin Musulunci, Malam Engr. Imrana Usman ya ƙalubalanci malamin yana mai bayyana cewa akwai tarin ƙarairayi a ciki.
Ya ce, a matsayinsa malamin addini bai kamata ya riƙa zuga mutane ga adawa ba, domin musulunci ya hana hassada da ƙiyayya da shiga shara ba shanu, yana mai bayyana shi a matsayin mai tallata ɗan siyasarsa kawai ba wai faɗar gaskiya ba.
Batun adawa da cewa a bai wa Sarakuna mulki ya ce, ai Imam Bashir shi ne ya fara yi wa Sarkin Musulmi tawaye ya nuna masa ƙiyayya a kan ganin wata, abin da ma ya haɗa shi da Izala kenan.
Game da sukarsa ta cewa mai aka yi wa Malamai a Kebbi da azumi, Engr. Imrana ya ce ana ta rabawa Masallatai 700,000 cikin azumi, waɗanda ma ba su samu ba yana kan hanya.
A kan gina Masallatai kuma, ya ce su masu addini sun san an yi ayyuka, domin gwamnatin ta gyara da gina Masallaci fiye da 150.
Kuma Masallacin da aka kori Imam Bashir bayan ya zagi Sarkin Musulmi yana cikin masallatan da Gwamnatin ta gyara ta sanya musu Solar.
Ya lissafo masallatai da dama da ya ce Gwamnatin ta gyara.
Dangane da ayyuka da ya ce Gwamnatin Kebbi ba ta yi Engr. Imran ya ce ƙanzon kurege ne domin Gwamnan Kebbi ya yi ayyuka lungu da saƙon jihar.
Game da adduʼoʼin da Malam Kabiru Gombe ya yi wa Gwamnan ya bayyana Imam Bashiru a matsayin mai yin hassada da ƙiyayya kawai.
A kan ceto ɗaliban Maga kuwa, ya ce malamin ya sani ko yana so ko baya so dole ne a yaba wa Gwamnatin tarayya da ta jihar Kebbi kan ƙoƙarinsu a kai, sannan a ƙarshe ya ce yana yi masa nasiha da ya ji tsoron Allah,





