Gwamnatin Kebbi ta kara jaddada goyon baya ga hukumomin tsaro

Gwamnatin Kebbi ta kara jaddada goyon baya ga hukumomin tsaro
 

 

 

Gwamnatin Jihar Kebbi ta sake jaddada kudirinta na ci gaba da tallafawa dukkan hukumomin tsaro da ke yakar ‘yan bindiga da ta’addanci a  jihar.

 
Kwamishinan yaɗa labarai da al’adu na Jihar  Alhaji Yakubu Ahmed Birnin Kebbi, ne ya tabbatar da hakan lokacin da ya karɓi Daraktan Yaɗa Labaran Sojoji, Birgediya Janar T. I. Gusau, wanda ya kai masa ziyarar ban girma a ofishinsa da ke Birnin Kebbi.
 
Alhaji Yakubu ya bayyana irin muhimman tallafin da Gwamna Nasir Idris ke bayarwa tun daga lokacin da ya hau mulki shekaru biyu da suka gabata, wanda ya haɗa da kayayyakin aiki, alawus da kuma bayanan sirri ga jami’an tsaro. 
 
Ya ce gwamnatin za ta ci gaba da ɗaukar nauyi domin ƙara ƙarfafa ƙoƙarin yaki da ‘yan bindiga.
 
Ya kuma shawarci hidikwatar tsaro da ta shirya taron tattaunawa tare da manyan masu ruwa da tsaki kamar sarakunan gargajiya, shugabannin addini, shugabannin al’umma da ƙungiyoyin matasa domin samar da haɗin kai da zai taimaka wajen samar da bayanan sirri ga jami’an tsaro.
 
Kwamishina ya kara da cewa ma’aikatarsa a shirye take ta yi aiki tare da sashen yada labaran sojoji wajen shirya wannan taro, domin amfani da tasirin shugabannin gargajiya wajen samun goyon bayan jama’a.
 
A nasa jawabin, Birgediya Janar Gusau ya shaida wa kwamishinan cewa ya zo jihar tare da tawagarsa domin ganin tasirin haɗin gwiwar da suka shiga da wasu kafafen yada labarai, wanda manufarsa ita ce ƙarfafa dangantaka tsakanin sojoji da al’umma wajen yaƙi da ‘yan bindiga a Jihar Kebbi da ma Arewa maso Yamma baki ɗaya.
 
Ya jaddada muhimmancin haɗin kai tsakanin jami’an tsaro da jama’a a dukkan wuraren da ake yaƙi da miyagun laifuka. Haka kuma, ya yaba wa Gwamna Nasir Idris bisa irin goyon baya mara yankewa da yake bayarwa ga rundunar sojoji, yana mai cewa hakan ya taka muhimmiyar rawa wajen nasarorin da aka samu har zuwa yanzu.
 
Birgediya Janar Gusau ya kuma isar da sakon godiyar Shugaban Hafsoshin Tsaro, Janar Christopher Musa, ga Gwamnatin Jihar Kebbi bisa jajircewarta wajen ganin an dawo da zaman lafiya a Jihar Kebbi musamman da kuma yankin Arewa maso yamma baki ɗaya.