Gwamnatin Katsina za ta baiwa kowace karamar hukuma Naira miliyan 20 don gyaran makabarta

Gwamnatin Katsina za ta baiwa kowace karamar hukuma Naira miliyan 20 don gyaran makabarta

Gwamnatin Jihar Katsina ta amince da kashe Naira miliyan 20 ga kowace karamar hukuma domin gyaran makabarta. 

Gwamna Dikko Radda ne ya bayyana haka yayin ganawarsa da sarakunan gargajiya daga masarautun Katsina da Daura.

Radda ya kuma sanar da sabon tsarin tallafi ga sarakunan gargajiya da malaman addini, inda dukkanin Hakimai za su karɓi albashi daga matakin na 16 zuwa sama, masu unguwanni 6,652 da limamai sama da 3,000 za su samu alawus na wata-wata.

 Haka kuma, masu tsabtace masallatai a kowace karamar hukuma za su amfana da tallafi.

Ya jaddada cewa tsaro shi ne fifikon gwamnatinsa, tare da bayyana cewa matasa fiye da 1,500 aka horas don tallafa wa jami’an tsaro.

Sarakunan gargajiya sun yaba wa gwamnan bisa sauye-sauyen da suka dawo da martabar masarautu tare da tabbatar da goyon bayansu wajen tabbatar da zaman lafiya da ci gaban jihar.