Home Labarai Gwamnatin Kano ta ce Sarki Muhammad Sanusi ne zai yi Hawan Sallah

Gwamnatin Kano ta ce Sarki Muhammad Sanusi ne zai yi Hawan Sallah

3
0

Gwamnatin Kano ta ce Sarki Muhammad Sanusi II ne zai yi Hawan Sallah

Gwamnatin Jihar Kano karkashin jagorancin Abba Kabir Yusuf ta fitar da sabbin tsauraran matakai kan bukukuwan Sallah domin kauce wa rikici da tabbatar da zaman lafiya.

A cikin sanarwar da Kwamishinan Yaɗa Labarai na jihar Ibrahim Abdullahi Waiya ya fitar, gwamnatin ta ce ta samu sahihan bayanan sirri daga Kwamitin Tsaro na Jihar da ke nuna yiwuwar wasu su haddasa rikici yayin bukukuwan Sallah a jihar.

Bayan tattaunawa da Majalisar Masarautar Kano, gwamnatin ta amince da cewa Hawan Idi zai gudana karkashin jagorancin Sarkin Kano, Muhammad Sanusi II, daga Kofar Mata zuwa fadar sarki ta Kofar Fatalwa, yayin da Hawan Nasarawa zai gudana amma ba tare da hawa dawakai ba.

Sai dai gwamnati ta sanar da dakatar da Hawan Daushe, Hawan Fanisau da Hawan Dorayi na wannan Sallah, domin kare lafiyar jama’a da tabbatar da tsaro.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here