Gwamnatin jihar Neja ta bi umarnin kotu ta rantsar da ciyaman din karamar hukuma na NNPP

Gwamnatin jihar Neja ta bi umarnin kotu ta rantsar da ciyaman din karamar hukuma na NNPP

Gwamnan jihar Neja, Sani Bello, ya rantsar da dan takarar jam’iyyar New Nigeria People’s Party, NNPP, Abdul-Alim Abubakar, a matsayin sabon shugaban karamar hukumar Gurara.

Rantsar da Abubakar ya biyo bayan umarnin wata babbar kotun jihar Neja, wacce ta soke zaben dan takarar jam’iyyar APC, Yusuf Walid.

An ayyana Walid a matsayin wanda ya lashe zaben kansiloli da aka yi ranar 10 ga Nuwamba, 2022.

Sai dai nasarar tasa ta fuskanci kalubale daga wani dan jam’iyyar, Saudaki Abubakar, wanda ya soki zaben shugaban da kotu ta tsige a matsayin dan takarar da aka amince da shi.

Da ta ke yanke hukunci, alkaliyar kotun,  Maimuna Abubakar, ta amince da wadanda suka shigar da karar sannan ta soke zaben fidda-gwani da aka gudanar.

Don haka kotun ta umurci hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar Neja da ta ba dan takarar jam’iyyar NNPP takardar shaidar lashe zaben, tunda shi  ya zo na biyu a zaben.

Da ya ke jawabi yayin bikin rantsar da ciyaman din a gidan gwamnati da ke Minna a yau Litinin, gwamnan, wanda ya samu wakilcin mataimakinsa, Ahmed Ketso, ya ce gwamnatinsa za ta ci gaba da mutunta doka, da kuma kishin jama’a a kowane lokaci.

Ya kuma bukaci sabon Ciyaman ɗin da aka rantsar da ya ba da fifiko kan tsaro da walwalar al’ummarsa.