Gwamnatin Gombe ta ɗauki ma’aikatan lafiya 451 aiki

Gwamnatin Gombe ta ɗauki ma’aikatan lafiya 451 aiki
 

Gwamnatin jihar Gombe ta ɗauki ma’aikatan lafiya 451 aiki domin bunƙasa harkar lafiya domin samun ingantaccen aiki.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Ismaila Misili, kuma ya bayyanawa manema labarai a Gombe a yau Asabar.

Ya ce jami’an da aka dauka sun hada da Ungozoma 106, Ma’aikatan Lafiyar Al’umma, CHEW 213 da kuma Kananan Ma’aikatan Lafiyar Al’umma, JCHEW, 132 wadanda za a tura su cibiyoyin kiwon lafiya a matakin farko a fadin jihar.

“Wannan na zuwa ne sabo da gwamnatin yanzu ta Gwamna Inuwa Yahaya ta yi imanin cewa kiwon lafiya a matakin farko shine tushen tsarin kiwon lafiya,” in ji shi.

Ya bayyana cewa gwamnati mai ci ta ba da fifiko ga harkokin kiwon lafiya da walwalar ƴan jihar, don haka aka samu dimbin nasara a bangaren.

Ya ce daukar ma’aikata wata gagarumar nasara ce a tarihin wannan fanni a jihar, baya ga fara ɗaukar horo na kwararrun ɗaliban fannin lafiya a asibitin kwararru da kuma ɗaukar manyan kwararrun harkar lafiya aiki.

Misili ya ce fara ba da horon da kuma ci gaba da gina sabuwar kwalejin koyon aikin jinya da ungozoma da ke Gombe duk an yi amfani da su ne domin bunkasar ma’aikata a fannin lafiya.