Gwamnan jihar Sakkwato Ahmad Aliyu ya ƙaddamar da shirin ciyarwa Azumin bana na shekarar 2026, ya ƙara tabbatar da gwamnatinsa za ta taimaki marasa ƙarfi a watan Ramadan.
A ƙaddamar da shirin a gidan tarihi cikin birnin Sakkwato a Lahadi da ta gabata Gwamnan ya bayyana hakan na cikin ginshiƙin taimakon mutane da ake yi don sauƙaƙa masu a lokacin watan Ramadan in da ake son samun haɗin kai da jinƙai a tsakanin Musulmai, musamman marasa ƙarfi.
A shekara da ta gabata a shirin an samar da cibiyoyi 155 da wasu ɗaiɗaiku 300,mutane suna buƙatar ƙara yawan cibiyoyi kan haka aka ƙara su zuwa 170 a wannan shekara kowace cibiya za ta iya ɗaukar mutum 200 a rana.
A cewar Gwamna naira biliyan ɗaya da aka ware a shirin zai samar da filate dubu 34 na abinci a kullum daga farko har ƙarshen azumi,abinci mai inganci da kowa zai iya cinsa a ko’ina.
Haka gwamnati ta samar da ma’aikatan wuccin gadi da za su yi aikin haɗa abincin.
Mutanen jiha suna ɗaura lamrrin a matsayin almubazaranci da dukiyar jama’a.
Aliyu Muhammad ya ce bai kamata gwamnati na wasa da dukiyar jama’a ba, wannan lamarin na ciyarwa ba ana yi ne don mutane ba sai don biyan buƙatar kansu.
Ya ce mutanen jiha ba su zuwa cin abinci a cibiyoyin daga almajirai sai ‘yan gudun hijira ne ke zuwa wurin.






