Gwamnan Zamfara Ya Bada Umarnin Buɗe Layukan Sadarwa A Ranar  Talata

Gwamnan Zamfara Ya Bada Umarnin Buɗe Layukan Sadarwa A Ranar  Talata


Daga Hussaini Ibrahim.

Gwamnan Jihar Zamfara  Bello Matawalle ya bi sahun gwamna Jihar Kaduna Malam Nasiru wajan bada Umarnin Bude layukan Sadarwa da ke fadi jihar baki daya da suka kwashe tsawon wata biyu da rabi da daukewar layukan Sadarwa Sabo da matsalar 'Yan Bindiga da masu garkuwa da mutane.

Matawalle ya bayyana haka ne a Taron zabar sabbin Shugabani na jam'iyyar APC na Jihar a Yau Asabar.

'kuma ya bayyana cewa, sakamakon sauki da aka samu na matsalar 'Yan Bindiga ya sanya bada Umarnin Bude layukan Sadarwa daga nan zuwa ranar talata mai zuwa.kuma wannan zaiba wanda bai yanki katin zabe ba,damar mallakar katin zaben. inji gwamna Matawalle.

Idan ba a mantana aranar Asabar 4/9/2021 , Gwamna Matawalle ya bada Umarnin rufe layukan Sadarwa dan samun damar yima Yan Bindiga kofarago dan gamawa dasu.