Home Manyan Labaru Gwamnan Sakkwato zai tallafawa ‘yan kasuwa su bunkasa kasuwancinsu

Gwamnan Sakkwato zai tallafawa ‘yan kasuwa su bunkasa kasuwancinsu

10
0

Gwamnan Sakkwato Dakta Ahmed Aliyu ya yi alkwalin samar da karin jari domin tallafawa ‘yan kasuwa bayan an kammala gyaran wani gefe na babbar kasuwa da ya kone shekarru da suka gabata. 

Ya sanar da alkawalin ne a lokacin da yake karbar ‘yan kasuwa domin bshan ruwa a babban dakin taro na masaukin shugaban kasa da ke Sakkwato.

Gwamna Aliyu ya godewa ‘yan kasuwar kan hankurinsu da fahimtarsu ga cigaba da goyon bayan gwamnatinsa, ya ba su tabbacin gwamnati za ta ci gaba samr da aiyukkan da za su kawata birnin Sakkwato don karfafa harkokin kasuwanci.

Gwamna ya kara ba da tabbacin gwamnatinsa za ta kara walwalar ‘yan kasuwa da samar da yanayi mai kyau don gudanar da kasuwancinsu.

“Muna aiki tukuru na ganin Sakkwato ta zama wata cibiyar ciniki da kasuwanci a yankin nan, wannan buri ba zai cika ba sai da hadin kai da goyon bayan ‘yan kasuwarmu,” a cewarsa.

Ya ce “gudunmuwarku nada muhimmanci ga kudirin da muke da shi, don haka nake rokon ku cigaba goya mana baya mu yi aiki tare don gina Sakkwato da za yi alfahari da ita.”

Shugaban ‘yan kasuwar jiha Alhaji  Chika Sarkin Gishiri ya godewa gwamna kan kwangilar gina wurin da ya kone a kasuwar Sakkwato, ya ba da tabbacin cigaba da goyon bayan gwamnati.

Tun a lokacin yekuwar zabe gwamnan ya yi alkawalin tallafawa ‘yan kasuwa in ya samu nasara abin da aka yi zaton a kwana 100 na farkon gwamnatinsa zai ware wasu kudi domin tallafawa ‘yan kasuwar amma ba a yi ba.

Wasu mutane a jiha suna ganin gwamna ya daure ‘yan kasuwa ne da igiyar zato domin neman goyon bayansu a zaben 2027 da ke tafe ne.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here