Gwamnan Sakkwato Zai Sayawa Kansa Motocin Hawa Na Biliyan Daya

Gwamnan Sakkwato Zai Sayawa Kansa Motocin Hawa Na Biliyan Daya

Gwamnan Sakkwato Dakta Ahmad Aliyu Sokoto zai Sayawa kansa  motocin hawa na naira biliyan daya da Miliyan daya.
Kwamishinan matasa Alhaji Jamilu Umar Gosta ne ya sanar da hakan ga manema labarai bayan kammala zaman majalisar zartarwa ta jiha a karo na uku.
Kwamishinan ya ce majalisar zartarwa ta aminta da sayawa ofishin Gwamna motocin alfarma na kimanin kudi naira biliyan 1 da Miliyan 1 da dubu 250, an ba da kwangilar ne ga Kamfanin mota na B. T.
Kwamishinan muhalli da gidaje Barista Nasiru Dantsoho ya ce gwamnatin za ta Gina hanyoyi a unguwar Runjin Sambo kan kudi naira Biliyan 2, za ta gina hanya kan titin  Bodinga(gaban gonar Alu) kan kudi sama da naira Miliyan 816.
Kwamishinan yada labarai Sambo Bello ya sanar da kudin da gwamnati ta ware Wanda aka kawata titin gidan gwamnati ya lakume kudi miliyan 488, hanyoyi 39 da aka kawata da hasken wuta Mai aiki da rana waton Sola ya lakume biliyan 1 da Miliyan 756.
Ya ce akwai wasu hanyoyin mota biyar da aka Kara za a a sanyawa fitillun aikin zai lakume Miliyan 97.
Haka ma majalisar zartarwa ta aminta da gina hanyoyi a unguwar Tudun wada Unguwar Rogo guda 47 kan kudi Biliyan 8 da Miliyan 999, za a kammala aiki a cikin shekara daya.
An Kuma bayar da hanyar Gande zuwa Silame kan kudi sama da Biliyan 2. Majalisa ta ware sama da Biliyan 18 domin wadannan aiyukkan.