Gwamnan Sakkwato ya amince da ba da Naira dubu 200 duk wata ga shugabannin makarantun sakandare
Gwamnan Sakkwato ya amince da ba da Naira dubu 200 duk wata ga shugabannin makarantun sakandare
Ciyarwa dalibbai a jiha ta mutu, da yawan makarantu ba su samu abinci wadatacce, kuma 'yan kwangila da ke kawo abincin suna biyar dimbin bashi ga gwamnati, da gwamna rage bashi ya rika yi da kudin, domin 'yan kwangilar ciyarwa su dawo da yafi, kuma shi ne abin da ake bukata da zai bunkasa ilmi saman baiwa shugabannin makaranta kudi.
Gwamna Ahmed Aliyu na jihar Sakkwato ya amince da baiwa ko wanne shugaban makarantar sakandare a jihar Naira dubu 200 a matsayin alawus a duk wata.
Ya baiyana hakan ne a wani taron sauraren kasafin kuɗi na 2025 a juya Litinin, inda ya ce za a baiwa dukkanin shugabannin makarantun sakandare a ƙananan hukumomi 23 na jihar.
Daily Trust rawaito cewa matakin ya zo ne bayan da wani tsohon mataimakin gwamna, Chiso Abdullahi ya bukaci hakan, inda ya nuna muhimmancin kyautata rayuwar shugabannin makarantun sakandare don inganta ilmi.
Wasu na ganin wannan tsarin ko an soma shi ba zai daure ba, domin a jihar akwai makarantun Sikandare sama da 400, wannan kudin ba karami ba ne kuma za su tafi a cikin aljihun shugaban makaranta.