Gwamnan Sakkwato na shan suka kan kwangilar gyaran bohol 25 a Kudi biliyan 1.2

Gwamnan Sakkwato na shan suka kan kwangilar gyaran bohol 25 a Kudi biliyan 1.2

 

Gwamnan Sakkwato Dakta Ahmad Aliyu na shan suka a jama'ar gari kan kwangilar da ya ayyana ya bayar na gyara rijiyoyin burtsatse 25 a wani bidiyo dake yawo a kafofofin sada zumunta.

Jama'a da dama sun tofa albarkacin bakinsu wasu karara sun bayyana kwangilar ta yi tsada wasu kuma sun yi shagube kan aikin.
Honarabul Abdullahi Hassan ya yi shagube kan kwangilar in da ya nemi mutanen jami'a su nema masa kwangilar gyaran bohol daya.
Bello Muhammad ya ce kwangilar gyara bohol daya kan kudi naira miliyan 48 ba abu ne da yake kama hankali ba yakamata gwamnati ta rika lura musamman a halin matsin rayuwa da ake ciki a kasar nan.
Ya yi kira ga gwamna ya rika duba halin da ake ciki mutanen da za a gyarawa bohol suna bukatar abinci da magani da hanya, kudin da aka ware a zaton da muke da shi suna iya samar da abu biyu a cikin abin da ake bukata, amma a kashe makudan kudin a gyaran bohol kamar an barnata kudin.
Kabiru Ahmad ya ce na kalli bidiyon, domin da aka fada min ban yarda ba, sai da gani da kaina a gaskiya wannan ita ce kwangila mafi tsada da nasani an bayar a gwamnati.
Ya ce ko samar da bohol da wuya ya  wuce a kashe naira miliyan 10, amma a ce za a yi gyara a miliyan 48 yakamata gwamnati ta lura a gaba, gaskiya nan an yi kuskure a tunanin da nake da shi.