Gwamnan Neja Zai Dauki Ma'aikatan Lafiya 1000

Gwamnan Neja Zai Dauki Ma'aikatan Lafiya 1000
 

Sakamakon ƙarancin ma'aikata a ɓangaren lafiya na jihar Neja, Gwamnati ta fara ɗaukar matakan gyara lamarin cikin gaggawa. Gwamnatin jihar Neja karkashin jagorancin Gwamna Umar Bago ta amince da ɗaukar sabbin ma'aikatan lafiya 1,000 da kuma maye gurbin waɗanda suka yi ritaya nan take. 

Kwamishinan lafiya na jiha, Dakta Ibrahim Dangana ne ya bayyana haka a Minna, babban birnin jihar Neja jiya Talata, kamar yadda Leadership ta tattaro. 
Ya ce gwamnatin gwamna Umar Mohammed Bago na daukar matakai ne domin tabbatar da an inganta bangaren kiwon lafiya da kuma samun rahusa a fadin jihar. Ya bayyana cewa babban kalubalen da ake fuskanta a fannin kiwon lafiya a jihar shi ne na karancin ma’aikata.
Kwamishinan ya ce za a cike giɓin da ke akwai a ɓangaren domin samar da kayan aikin kulawa da masu juna biyu, tsarin iyali da kuma gyara dangantakar asibitocin PHC a faɗin jihar. 
"Za a kafa tawagar da za ta sanya ido kan asibitocin matakin farko PHC da nufin gyara duk wani nau'i na ba daidai ba da ake aikatawa a ɓangaren lafiya, da kuma uwa uba cika muradan al'umma."