Gwamnan Neja ya gargaɗi al'umar jihar kan zuba shara a magudanun Ruwa, don yana haifar da ambaliya

Gwamnan Neja ya gargaɗi al'umar jihar kan zuba shara a magudanun Ruwa, don yana haifar da ambaliya

Gwamnan Neja ya gargaɗi al'umar jihar kan zuba shara a magudanun Ruwa, don yana haifar da ambaliya

A daidai lokacin da ake kwarara ruwan sama a jihar Neja, gwamna Abubakar Sani Bello ya gargadi jama'a da su guji zuba shara akan hanyar magudanan ruwa dan kaucewa ambaliyar ruwan sama.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a lokacin da yake rangadin ganin yadda magudanan ruwa suka kasance da ke janyo ambaliyar ruwan a sassan jihar.
Yace ya zama dole jama'a su kaucewa abinda zai janyo barna.
A cewarsa, ya kamata jama'a su kauracewa zubar da shara a magudanan ruwa domin shi ne musabbabin abinda ke janyo ambaliyar ruwan sama a jihar.
Haka gwamnan ya jawo hankalin jama'ar jihar da su daina toshe hanyoyin ruwa, tare da tabbatar sun tsaftace tare da barin hanyoyin da ruwa ke wucewa.
Gwamnan ya umurci ma'aikatar muhalli ta jiha da ta tabbatar duk wani sharan da aka zuba a magudanan ruwa sun kwashe shi, yayi kira ga al'ummomi musamman matasa da su tabbatar suna sanya idanu akan tsaftace magudanan ruwa.
Gwamnan ya umurci ma'aikatar ayyuka ta jiha da su samar da hanyar ruwa a yankin unguwar Fadikpe dan daukar matakin gaggawa a yankin ganin yadda ruwan sama ke ambaliya a gidajen jama'a saboda rashin hanyar wucewar su.