Gwamnan Nasarawa Ya Yi Alkawalin Kujerar Gwamna Kawai Zai Rika a Siyasa

Gwamnan Nasarawa Ya Yi Alkawalin Kujerar Gwamna Kawai Zai Rika a Siyasa

Gwmnan Nasarawa Abdullahi Sule ya ce ba shi da sha'awar sake neman wani muƙamin siyasa bayan ya kammala wa'adinsa na biyu a matsayin gwamnan.

Cikin wata tattaunawa da ya yi da Channels TV a ranar Juma'a kan nasarar da ya samu a kotu koli game da zaɓen gwamnan jihar.

An share awanni ana zanga-zanga a Nasarawa a jiya Juma'a, bayan tabbatar da shi da kotun ta yi a matsayin zaɓabben gwamnan jihar Nasarawa.

Ya ce "Ni matsyin gwamnan kawai na zo na rike, ba ni da shirin zama shugaban jam'iyya ko kuma Sanata ko ɗan majalisa ba ni da wani burin siyasa a nan gaba."

Gwamnan ya yi alkawalin kujerar gwamna kawai zai rika a siyasa abin da ake ganin zai yi matukar wahala gare shi ganin yanda Gwamnoni ke fadi tashin ganin sun samu wasu kujerun mulki bayan kammala wa'adin mulkinsu.

A siyasar Nijeriya akwai tsaoffin Gwamnoni da tun sanda suka ajiye mukamin Gwamna ba su sake neman kowace kojera ba amma dai su ne kadan bisa ga wadan da ke son a cigaba da jin sunan su a harkokin siyasar Nijeriya.