Gwamnan Nasarawa ya sauke Kwamishinoninsa gaba ɗaya

Gwamnan Nasarawa ya sauke Kwamishinoninsa gaba ɗaya
Gwamnan Nasarawa ya sauke Kwamishinoninsa gaba ɗaya

Gwamnan jihar Nasarawa Injiniya Abdullahi Sule  ya saukar da kwamishinoninsa wanda suna cikin  ‘yan majalisar zartaswar jihar.

Gwamnan da kansa ya ba da sanarwar sauke ‘yan majalisar a yau Laraba bayan wani taro na masu ruwa da tsaki a Fadar Gwamnatin Jihar da ke Lafia.
Wannan mataki ya shafi har da masu bai wa Gwamna shawara da sauran masu muƙaman siyasa.
Gwamna Sule ya yaba wa kwamishinonin da hadiman da ya sauke bisa gudunmawarsu da suka bayar wajen cigaban gwamnatinsa da ma jihar baki ɗaya.

Gwamnan bai yi wani bayani kan sauke muƙaraban ba amma dai wasu na ganin wannan nada nasaba da 2023.