Home Siyasa Gwamnan Kebbi ya rushe shugabancin hukumar zaɓe ta jiha

Gwamnan Kebbi ya rushe shugabancin hukumar zaɓe ta jiha

4
0

Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya amince da rushe kwamitin gudanarwa na Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Jihar Kebbi, KEBSIEC, biyo bayan ƙarewar wa’adin mambobinta.

Gwamnan ya amince da rushe kwamitin ne daga ranar 18 ga Satumba, 2026, kamar yadda wata sanarwa da aka rabawa manema labarai a ranar Talata, 8 ga Satumba, 2026, ta bayyana.

Sanarwar wadda Sakataren Gwamnatin Jihar Kebbi, Alhaji Yakubu Bala Tafida, ya sanya wa hannu, ta ce an ɗauki matakin ne sakamakon ƙarewar wa’adin mulkin kwamitin gudanarwar hukumar.

A cewar sanarwar, Gwamna Nasir Idris ya nuna godiya da jinjinawa mambobin kwamitin da ke barin muƙamansu bisa gudummawar da suka bayar wajen gudanar da ayyukan hukumar da kuma hidimar da suka yi wa jihar a lokacin da suke kan muƙamansu.

A wata sanarwa da Babban Sakataren Yada Labarai na Gwamnan Jihar Kebbi, Ahmed Idris, ya fitar a ranar talata.

Gwamnan ya kuma jaddada cewa gwamnatinsa na da ƙudirin tabbatar da ’yancin kai da mutuncin Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Jihar Kebbi, domin ta samu damar gudanar da ayyukanta yadda ya kamata.

A cikin sanarwar, Gwamna Idris ya tabbatar wa hukumar cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da kare matsayinta na hukuma mai zaman kanta.

Rushewar za ta fara aiki ne daga ranar 18 ga Satumba, 2026, yayin da ake sa ran za a sake kafa sabon kwamitin domin ci gaba da jagorantar ayyukan hukumar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here