Gwamnan Kebbi ya karɓi jagororin PDP da magoya bayansu a Zuru cikin jam’iyyar APC

Gwamnan Kebbi ya karɓi jagororin PDP da magoya bayansu a Zuru cikin jam’iyyar APC
Gwamnan Jihar Kebbi, Kwamared Dr. Nasir Idris, Kauran Gwandu, a ranar Laraba ya karɓi manyan jiga-jigan jam’iyyar PDP da daruruwan magoya bayansu waɗanda suka sauya sheƙa zuwa jam’iyyar APC a Zuru.
Wannan sauya sheƙa da dama yana nuni da babban ci gaba ga jam’iyyar APC a Jihar Kebbi.
Daga cikin fitattun waɗanda suka sauya sheƙa akwai Alhaji Saleh Gambo, sanannen ɗan kasuwa, da Alhaji Lawali Dagolo, tsohon Mataimakin Shugaban jam’iyyar PDP a Jihar Kebbi.
Wadanda suka sauya sheƙar sun bayyana salon shugabanci na adalci da haɗin kai da Gwamna Idris ke yi, tare da ayyukan raya ƙasa da suka shafi jama’a a faɗin jihar, a matsayin dalilin sauya sheƙarsu zuwa jam’iyyar mai mulki.
Da yake magana a madadin tawagar, Alhaji Saleh Gambo ya sha alwashin biyayya mara yankewa ga Gwamna Idris tare da alkawarin yin aiki tukuru domin nasarar gwamnatinsa.
A nasa jawabin, Sanata Garba Musa Maidoki wanda ya shirya sauya sheƙar, ya shaidawa Gwamnan cewa, da ficewar waɗannan manyan mutane daga PDP, jam’iyyar a masarautar Zuru ta raunana sosai kuma yanzu babu wani jagoran siyasa da za a dogara da shi.
Shima da yake jawabi, Shugaban jam’iyyar APC na Jihar, Alhaji Abubakar Kana-Zuru, ya tarbi sababbin ‘ya’yan jam’iyyar hannu bibbiyu, tare da tabbatar musu da adalci da cikakken haɗa su da tsarin jam’iyyar.