Gwamnan Kano ya yi watsi da mu duk da gudunmawar da mu ka bayar a zaɓe -- Ƴan kasuwa

Gwamnan Kano ya yi watsi da mu duk da gudunmawar da mu ka bayar a zaɓe -- Ƴan kasuwa
 
Ƴan kasuwa a Kano sun koka da cewa gwamnan jihar, Abba Kabir Yusuf ya yi watsi da su tun bayan da ya lashe zaɓen 2023.
 
Ƴan kasuwan, ta bakin Munzali Abubakar Dambazau, wanda shi ne jagoran ƙungiyar Abba na Kowa a Kano, ya ce tuni ƴan kasuwa, musamman na kasuwar Kantin Kwari su ka fara gunaguni kan cewa gwamnan ya yi watsi da su.
 
Da ya ke magana a shirin Kowanne Gauta na Freedom Radio, Dambazau ya ce, a lokacin zaɓen gwamna sanya gabata, ƴan kasuwar Kwari sun bada gudunmawar atamfuna da shaddoji da kudade don ganin Abba ys samu nasara, inda ya kara da cewa "lamarin na neman zama cewa mun tura mota amma ta bule mu da hayaƙi."
 
"Yan kasuwa da dama su na ƙorafi. Mu ne mu ke tare da su kuma mu ne wakilan gwamna a kasuwanni, dole ne idan muka ji ko mu ka ga wani abu na ba dai-dai ba dole mu jawo hankalin mai girma Gwamna.
 
"Mu na kira ga gwamna da Jagora, Dakta Rabi'u Musa Kwankwaso, da su dubi yan jam'iyya, musamman ƴan kasuwa da ya cika alkawaran da ya daukar wa ƴan kasuwa, musamman ma kasuwar Kwari.
 
"Shi ya sa mu ke kira ga gwamnan Abba mai adalci da ya saurari koken nan na dubban ƴan kasuwa a jihar Kano," in ji Dambazau.