Gwamnan Kano ya mayarwa da Ganduje martani kan zaben 2027
Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano ya baiyana cewa jam'iyyar NNPP mai mulki a jihar ba za ta razana da duk wata barazana da tsohon gwamnan jihar, Abdullahi Umar Ganduje ke yi kan zaɓen 2027 ba.
Daily Trust ta tuna cewa Ganduje ya sha alwashin kwace mulkin Kano daga hannun NNPP a zaben shekarar 2027 mai zuwa.
Ganduje na bayani ne ta bakin shugaban jam'iyyar APC na Kano , Abdullahi Abbas a yayin taro da tsoffin 'yan majalisa ta 8 da ta 9 a jihar Kano.
Sai dai da ya ke mayar da martani a jiya Laraba a wajen rabon tallafi ga nata 5, 200, Gwamna Yusuf ya ce, “Bari na fada muku, duk wanda ya yi wa mutanen Kano barazana zai fuskanci matsala. Mu a shirye muke, kuma ba zan yi kasa a gwiwa ba don daukar kwakkwaran mataki a kan sa.
“Masu maganar karbar mulki a 2027, bari in tunatar da ku, mulki na Allah ne. Shi ne ke ba da shugabanci, kuma mu na addu’ar Allah Ya ba wa wanda ya fi kowa alheri ga mutanen Kano.
“Ba wai zaben 2027 mu ka mayar da hankali a kai ba, abin da mu ka sa a gaba shi ne mu cika alkawarin da mu ka daukar wa al’ummar Kano mu kuma sauke nauyin da su ka dora mana.
"Manufarmu ita ce mu ci gaba da samar da ribar dimokuradiyya tare da yi wa al’ummarmu hidima .
“Allah Ya ba mu ƙarfi da ikon cika wannan, mu kuma kai shekarar 2027 cikin koshin lafiya", inji Gwamnan.
managarciya