Gwamnan jihar Katsina, Dikko Radda ya yi haɗari a mota a kan titin Katsina zuwa Daura a jiya Lahadi.
A wata sanarwa da Sakataren Yaɗa Labaran gwamnan, Ibrahim Kaula Mohammed ya fitar, ya ce haɗarin ba mummunan ba ne kuma Radda ya samu ƙanƙanin rauni a jikin sa.
Ya ce lamarin ya faru ne lokacin gwamnan na dawowa daga Daura zuwa garin Katsina bayan kammala wani aiki na al’umma.
A cewar Mohammed, gwamnan na cikin koshin lafiya bayan ya samu agajin gaggawa daga likitoci kuma ya godewa al’ummar jihar bisa goyon baya da addu’o’i da su ke yi wa gwamnan.





