Gwamnan jihar Katsina, Radda ya yi haɗari a mota
Gwamnan jihar Katsina, Dikko Radda ya yi haɗari a mota a kan titin Katsina zuwa Daura a jiya Lahadi.
A wata sanarwa da Sakataren Yaɗa Labaran gwamnan, Ibrahim Kaula Mohammed ya fitar, ya ce haɗarin ba mummunan ba ne kuma Radda ya samu ƙanƙanin rauni a jikin sa.
Ya ce lamarin ya faru ne lokacin gwamnan na dawowa daga Daura zuwa garin Katsina bayan kammala wani aiki na al'umma.
A cewar Mohammed, gwamnan na cikin koshin lafiya bayan ya samu agajin gaggawa daga likitoci kuma ya godewa al'ummar jihar bisa goyon baya da addu’o’i da su ke yi wa gwamnan.
managarciya