Gwamnan Bauchi Ya Gabatar Da Sama Da Naira Biliyan 465 Kasafin Kudin 2025

Gwamnan Bauchi Ya Gabatar Da Sama Da Naira Biliyan 465 Kasafin Kudin 2025

Gwamnan jihar Bauchi, Bala Muhammad a ranar Alhamis ya gabatar da kasafin kuɗin 2025 da yawansa ya kai Naira Biliyan 465,805,248,317.12 ga majalisar dokokin jihar Bauchi domin nazari da neman amincewa.

Da ya ke gabatar da kasafin, gwamnan ya jinjina wa irin haɗin kai da ake samu a tsakanin majalisar dokokin jihar da bangaren zartarwa na jihar wanda ya misalta hakan a matsayin hanyar ciyar da jihar gaba.

A cewar Gwamnan, Naira biliyan 283.8 ne aka ware a matsayin hasashen kuɗin da za a kashe a ɓangaren manyan ayyuka wato kaso 60.7 cikin 100 na kasafin na shekarar baɗi.
 
Yayin da kuma sauran kaso 39.3 aka ware domin gudanar da ayyukan yau da gobe. Sai ya nemi haɗin kan majalisar wajen ganin ta gudanar da ayyukan ta da wuri domin amincewa a kan lokaci, lamarin da zai taimaki gwamnatin wajen gudanar da ayyukan da aka tsara aiwatarwa a shekara mai zuwa.

Shi kuma a nasa ɓangaren bayan karɓar kundin kasafin, Kakakin majalisar dokokin jihar Bauchi, Rt. Hon. Abubakar Y Sulaiman, ya yi alƙawarin cewa, mambobin majalisar za su bibiyi kundin kasafin a tsakanake domin hanzarin amincewa da shi.

Ya nemi rassa da hukumomin gwamnatin jihar da su mutunta gayyatar kwamitocin majalisar domin kare kasafin ma’aikatun su domin sauƙaƙa wa majalisar ayyukan nata don ganin an amince da kasafin a kan lokaci.