Gwamna Wike Ya Yi Martani Ga Buhari Kan Hana Amfani Da Naira 1000 Da 500

Gwamna Wike Ya Yi Martani Ga Buhari Kan Hana Amfani Da Naira 1000 Da 500

 

Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, ya soki matakin shugaban kasa, Muhammadu Buhari, na haramta amfanin tsoffin takardun N500 da N1000 a jawabinsa na ranar Alhamis. Wike ya ce kuskure ne shugaba Buhari ya yi haka duk da umarnin Kotun koli wanda ya bayyana cewa dukkan takardun naira su ci gaba da amfani har zuwa lokacin da zata yanke hukuncin ƙarshe. 

Channels tv tace gwamnan Ribas ya faɗi haka ne yayin hira da kafafen watsa labarai jim kaɗan bayan jawabin da shugaban kasa ya yi kai tsaye ga yan Najeriya ranar Alhamis. 
Ya ayyana matsayar Buhari ta halatta amfani da N200 da kuma haramta N500 da N1000 da, "Katsalandan" inda ya ce: 
"Tun da Kotun koli ta ba da umarnin cikin shari'a ya kamata mu jinkirta zuwa lokacin. A iya abinda na sani wannan shiga sharo ba shanu ne wanda ba abu ne mai kyau ba ga tsarinmu, Dimukraɗiyyar mu." 
Wike ya ƙara da cewa duk da an ɓullo da tsarin sauya naira ne da nufin wasu mutane amma lokaci da kuma hanyar aiwatar da shi kuskure ne. Gwamnan Ribas ya ce ya yi tsammanin shugaban ƙasa Buhari zai yi biyayya ga Umarnin Kotun Allah ya isa, ba zai tsoma baki ba. 
"Kotu lamba ɗaya a kasar nan ta yi magana, Kotun koli tace karku yi wani abu da zai shafi amfanin tsoffin takardun kuɗi. 
Ina ganin (Kalaman shugaban kasa) bai dace ba kuma ban ji daɗi ba."