Gwamna Radda Ya Rantsar da Sabbin Kwamishinoni a Katsina

Gwamna Radda Ya Rantsar da Sabbin Kwamishinoni a Katsina

Gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, a ranar Talata, ya rantsar da sabbin kwamishinonin da majalisar dokokin jihar ta tantance tun farko. Babban mai taimaka wa gwamna kan harkokin digital midiya, Isah Miqdad ne ya tabbatar da haka a wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Tuwita. 
Bayan haka, gwamna Raɗɗa ya bai wa sabbin mashawarta na musamman guda 18 rantsuwar kama aiki a taron wanda ya gudana a filin wasan People Square ranar Talata. 
A jawabin da ya yi a wurin bikin rantsarwan, Radda ya ce galibin sabbin kwamishinonin mutanen mazaɓarsu ne suka zaɓe su bisa cancanta da kuma amana. 
Mutane suna cewa masu rike da mukamai a gwamnatinmu masu basira/fasaha ne, ina tabbatar muku da cewa dukkansu masu fasaha ne da kuma ’yan siyasa saboda mutanen mazabarsu ne suka mika sunayensu don nada su." Raɗda ya bukaci sabbin wadanda aka nada da su gudanar da ayyukansu da kwazo da jajircewa maimakon su riƙa binsa duk inda ya je domin gudanar da aikinsa.