Home Siyasa Gwamna Makinde da Kwankwaso suna ganawar sirri, ana hasashen shirin zaɓen 2027

Gwamna Makinde da Kwankwaso suna ganawar sirri, ana hasashen shirin zaɓen 2027

2
0

Seyi Makinde, gwamnan jihar Oyo, ya gana a sirrance da jagoran jam’iyyar NNPP, Rabiu Musa Kwankwaso, lamarin da ya tayar da ce-ce-ku-ce kan yiwuwar sabon tsarin haɗin gwiwar siyasa gabanin zaɓen shekarar 2027.

Rahotanni sun nuna cewa ganawar ta gudana ne a bayan ƙofofi rufe, inda ba a bayyana cikakken abin da aka tattauna ba.

Sai dai masana harkokin siyasa na ganin cewa irin wannan ganawa tsakanin manyan ‘yan siyasa daga jam’iyyu daban-daban na iya kasancewa wata alama ta shirye-shiryen kawance ko sabuwar tafiya a siyasar ƙasar nan.

Gwamna Makinde na cikin manyan jiga-jigan jam’iyyar PDP a Kudu maso Yamma, yayin da Kwankwaso kuma ke jagorantar NNPP tare da magoya bayansa na Kwankwasiyya musamman a Arewacin Najeriya.

Duk da cewa bangarorin biyu ba su fitar da wata sanarwa a hukumance ba kan abin da suka tattauna, ganawar ta jawo hankalin jama’a tare da ƙara zazzafar muhawara kan yiwuwar sauye-sauye a siyasar Najeriya kafin zaɓen 2027.

Yayin da siyasa ke kara dumama, ana sa ido ko wannan ganawa za ta haifar da wani sabon kawance a fagen siyasar Najeriya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here