Gwamna Mai Mala Buni Ya Gabatar Da Kasafin Kudin Shekara 2022 Na Naira Biliyan 164
Kasafin kudi na 2022 kasafin kudi da aka masa lakabi da kasafin kudi na cigaba da ayyukan da aka sanya gaba da kuma kokarin Samar da aikin yi.
Gwamnan ya kuma kara da cewa, kasafin kudi na shekarar da ta gabatar 2021 an cimma burin sa da wajen kashi 77 cikin dari wadda hakan ya nuna karara cewar kwalliya ta biya kudin sabulu.
Bangarorin da suka fi samun kaso mai tsoka sun hada da bangaren bangaren Gudanar da harkokin gwamnati da suka kunshi gidan gwamnati, bangaren sakataren gwamnati, ɓangaren shugaban ma'aikata da makamantan su, sun tashi da kimanin Naira Biliyan 56,941,840.
Bangaren ayyuka da gidaje shi ya zo na biyu da samun Naira Biliyan 29,840,294,000 ya tashi da kashi 18.2. Yayin da sashin Ilimi ya zo na Uku da samun kasafin Naira Biliyan 28,728,344 wato kashi 17.5 cikin Dari.
Gwamna Buni ya kuma jaddada kudirin gwamnatin sa na bada fifiko matuka kan abin da ya shafi Samar da hanyoyin mota a birane daa karkara wadda hakan zai sa harkokin sufuri ya inganta ta yadda al'umma za su samu sa'ida.
Ta bangaren ma'aikatan gwamnati kuwa, gwamnan ya bayyana cewar, duk da halin tattalin arziki da ya dabaibaye Jihar da gwamnatin tarayya hakan bai sa gwamnatin Jiha yin kasa a gwiwa ba wajen ci gaba da biyan albashi, kuma In Allah ya so za su ci gaba da biyan ma'aikata hakkokin su kamar yadda suka saba.
Tun farko da ya ke gabatar da gwamnan Kakakin majalisar dokokin Jihar ta Yobe Honarabul Ahmed Lawan Mirwa ya tabbarwa gwamnan Cewar, kasafin kudi za su duba shi kan lokaci don al'ummar Jihar su amfana
managarciya