Gwamna da jagoran APC a Sokoto sun karramani---Bello Yahaya Wurno

Gwamna da jagoran APC a Sokoto sun karramani---Bello Yahaya Wurno
 
Sabon shugaban gudanarwa a hukumar raya gulaben Rima Honarabul Bello Yahaya Wurno ya gabatarda takarda mukaminsa ga Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko domin sanya masa albarka a gidansa dake Gawon nama satin da ya gabata.
Honarabul Bello Yahaya bayan godewa Gwamnan Sakkwato da Sanata Wamakko kan rawar da suka taka a wurin samun mukaminsa ya ce "ina yi wa gwamnan Sakkwato Dakta Ahmad Aliyu da jagoran APC a jiha Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko da sauran wadan da suka yi min fatan alherin samun wannan mukamin sun karramani ina cewa na gode.
"Ina neman cigaba da addu'o'insu da goyon baya da hadin kai don sauke nauyin da aka daura min."
Yahaya Wurno ya ce zai mayar da hankali wurin ganin an  samar da abinci isasshe da rage talauci da samar da aikin yi da kawo cigaban tattalin arziki a kauyukka. 
"Za mu yi maraba da duk wata gudunmuwa da za ta kawo cigaba a tafiyar da hukumar(Sokoto Rima River Basin).
"Hukumar za ta yi tsaye ta tabbatar kudirin shugaban kasa ya tabbata kan haka masu ruwa da tsaki a jjihohin Sakkwato, Kebbi da Zamfara da Katsina da  hadin kanku za mu dawo da burin hukumar na samar da abinci, da aiki tare za mu kai hukumar in da ake bukata.