Gwamna Buni ba shi da laifi wajen faduwar APC a zaben Shugaban kasa a Yobe- Engr Umar Ali

Gwamna Buni ba shi da laifi wajen faduwar APC a zaben Shugaban kasa a Yobe- Engr Umar Ali

Daga Muhammad Maitela, Damaturu.

An bayyana cewa rashin wakilci nagari, ta fuskar yan majalisar dokokin Yobe, Shugabanin kananan hukumomi, tare da wakilan al'umma a matakai daban-daban a matsayin tarnakin da ya dabaibaye jam'iyyar APC ta sha mummunan kaye, a zaben Shugaban kasa hade da na yan majalisun a makonnin da suka gabata a jihar Yobe. 

Wannan furucin ya fito ne daga bakin dan takarar Gwamnan jihar Yobe a karkashin jam'iyyar APC da NNPP a zabukan fidda-gwani na shekarar 2019 da 2022, Engr. Mallam Umar Ali, wanda halin yanzu na hannun daman Gwamnan jihar Yobe ne, Hon. Mai Mala Buni, a wani taron tuntuba da ya gudanar da magoya bayansa, a babban dakin taron karamar hukumar Bade da ke Gashu'a a jihar Yobe. 

Taron wanda ya tattaro mata da matasa a kananan hukumomi 6 dake Yobe ta Arewa (Zone C), domin jin korafe-korafen jama'a tare da daukar matakan shawo kan su, ta hanyar bai wa gwamnatin jihar Yobe muhimman shawarwari don neman mafita. 

Biyo bayan abubuwan da suka faru ne a lokacin zaben ne ya jawo cewa ya kamata a matsayin su na mukarraban Gwamna Buni su zauna wajen nazarin gano mafita ga matsalolin da suka jawo faduwar jam'iyyar APC a zaben Shugaban kasa. Ya ce, "Saboda a tarihin jihar Yobe ba a taba samun lokacin da jama'a suka yi fishi, sun yi bore ba zasu fito zabe ba ko kuma ba zasu zabi APC ba, sai a wannan karo."

Ya ce idan hakan ya faru dole akwai dalilai, saboda mutane ba su yi bore ba don basu son gwamnati, ko saboda basu son APC, face kawai jama'a sun dauki wannan matakin ne domin su nunawa gwamnati cewa akwai matsala don a gyara. 

"Kuma Gwamna da kansa ya ji wadannan korafe-korafen, inda hakan ya sa ya bukaci muji koken al'umma tare da bin hanyoyin gyara su, wanda gashi mun hadu da mutane kuma sun yi bayanai da kansu, kuma zamu isar da sakon su tare da bayar da shawarwari masu ma'ana don a gyara." 

"Bugu da kari, mun gano cewa wadanda suke wakiltar al'umma ne basu gudanar da wakilci mai kyau; basu isar da sakon al'umma irin yadda ya kamata. Wannan su ne korafe-korafen jama'a suke fada mana a dukan wuraren da muka ziyarta a fadin jihar Yobe."

Ya ce korafin da yafi yawa shi ne irin yadda yan majalisun dokoki da shugabanin kananan hukumomi, sun sani mutanen su basu da ruwan sha, babu wutar lantarki da hanyoyi a wasu wurare, amma ba za su kaiwa gwamnatin jihar koken al'umma ba, illa iyaka idan sun yi korfi sai matsalolin kansa ko na makusantan su.

Malam Umar ya ce, "Wadannan matasa, da mata sune kan gaba wajen jefa kuri'a, inda mata suke shiga gida-gida lungu da sako wajen nemo mata su fito jefa kuri'unsu, amma da zarar an gama zabe shikenan ba zasu sake ganin wakilan su ba, sai zabe ya zagayo. Su kuma matasa su ne masu kokari a lokacin zabe, su jefa kuri'a, su kasa su tsare kuma su raka, amma da zarar an bayyana sakamakon zabe, shikenan an bar su."

Engr. Umar Ali ya bai wa daruruwan mata da matasan hakuri tare da daukar alkawarin share musu hawayen su, "Nayi muku alkawarin zan gaya wa Gwamna Buni kokenku. Kuma ina mai jan hankalin matasa, mu natsu, saboda irin halin matsin tattalin arziki da ake ciki, babu yadda za a yi ace gwamnati ta ba kowanen mu aiki, kuma kar mu yarda da duk wanda zai mana dadin bakin yuwar hakan. Amma abin da za a yi shi ne duk lokacin da gwamnatin Yobe zata dauki ma'aikata, za mu shige muku gaba, mu tabbatar anyi adalci wajen saka sunan wasu daga cikin ku." 

Ya kara da cewa, idan gwamnati za ta bayar da tallafi ga jama'a, za su tsaya kan dole a raba zuwa kowa ya samu, ba tare da sun bari wasu sun handame wajen karkaar da tallafin zuwa tsiraru ba. Ya ce, "za mu bukaci a bamu dama mu shiga kowane lungu don haduwa da jama'a wajen nemo wadanda suka cancanta mu mika masa. Suma wakilan jama'a a basu wanda zasu kawo, amma zamu tsaya sai an tantance, wannan shi ne kudurinmu." 

"Muna kara baiwa jama'a hakuri a fito a zabi wannan gwamnati a karkashin jam'iyyar APC; mu tabbatar mun zabi Gwamna Mai Mala Buni tare da yan majalisar dokoki masu rinjaye wadanda zasu taimaka masa wajen ci gaba da gudanar da ayyukan ci gaba. Saboda idan muka yi kuskuren zabar wata jam'iyyar da ba APC ba, tamkar mun toshe wa kanmu kofar ci gaba ne a sama. Kuma muna da cikakkiyar damar da zamu kalubalance su."

A karshe Malam Umar Ali ya ja hankalin matasa su guji harkokin bangar siyasa kuma su guji hada hanya da baragurbin yan siyasa masu bai wa matasa miyagun kwayoyo don su yi amfani dasu a lokutan zavuka.