Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya gudanar da wata ganawar sirri da jagoran jam’iyyar NNPP kuma tsohon gwamnan jihar, Rabiu Musa Kwankwaso, a gidansa da ke Miller Road, Kano, gabanin tafiyarsa zuwa ƙasar Faransa domin ganawa da shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu.
Rahotanni da Daily Nigerian ta samu sun nuna cewa ganawar ta gudana ne a daren Talata, 6 ga Janairu, 2026. Majiyoyi sun bayyana cewa gwamnan ya isa gidan Kwankwaso da tsakar dare, cikin wata mota mai duhu.
Majiyoyi sun ce tattaunawar ta ɗauki sama da awa guda, amma bayanai sun nuna cewa gwamnan bai samu nasarar shawo kan Sanata Kwankwaso ba domin ya bi shi zuwa jam’iyyar APC, kamar yadda ake zargin akwai matsin lamba daga wasu manyan mutane.
Bayan kammala ganawar, washe gari, Sanata Kwankwaso ya yi jawabi ga magoya bayansa a gidansa, inda ya jaddada cewa ba shi da “farashi” a siyasa. Ya ce cin amana ba abu ne mai kyau ba, yana mai nuni da matsalolin tsaro da tattalin arziki da ke rage farin jinin jam’iyyar APC a idon jama’a.
“Wasu na cewa a Nijeriya kowa na da farashi. Idan kana neman wanda ba shi da farashi, ka zo wurin Rabiu Kwankwaso,” in ji shi.
Rahoton ya ce shirin gwamnan na sauya sheƙa zuwa APC ya fuskanci cikas bayan shugabannin jam’iyyar sun lura da martanin jama’a a Kano. Duk da cewa wasu ‘yan majalisar dokoki na NNPP a matakin jiha da ƙasa, da kuma wasu shugabannin ƙananan hukumomi, na shirin sauya sheƙa tare da gwamnan, mafi yawan magoya bayan NNPP a jihar sun ci gaba da nuna cikakken goyon baya ga Kwankwaso.
Wata majiya ta bayyana cewa shugabannin APC na sa ido sosai kan halin da ake ciki a Kano, inda magoya bayan Kwankwasiyya ke nuna karara cewa suna tare da Kwankwaso. Ta ce idan gwamnan ya shiga APC, akwai yiwuwar ɗan takarar da Kwankwaso ya goyi baya ya samu ƙuri’u masu yawa sakamakon ramuwar gayya.
Majiyoyi sun kuma ce Shugaban kaasa na ci gaba da yunƙurin ganin Kwankwaso ya shiga APC, abin da ya sa ake neman shawo kansa ta hanyoyi daban-daban.
Rahoton ya ƙara da cewa ana sa ran gwamnan zai gabatar wa Shugaban kasa cikakken bayani kan sakamakon ganawarsa da Kwankwaso, tare da tsara matakan tafiyar da al’amuran jam’iyya idan ya yanke shawarar sauya sheƙa.
A halin yanzu, manyan shugabannin APC a Kano, ciki har da tsohon gwamna Abdullahi Ganduje, mataimakin shugaban majalisar dattawa Barau Jibrin, shugaban jam’iyyar APC na jiha Abdullahi Abbas, da Nasiru Gawuna da Murtala Garo, sun dawo ƙasar nan bayan hutun ƙarshen shekara da aikin Umrah.
Ana sa ran Gwamna Abba Kabir Yusuf zai sanar da matsayinsa kan batun sauya sheƙa ne bayan kammala shawarwari da shugabannin APC a jihar.




