Gwamna 14 Ke Goyon Bayan Takarar Shugaban Kasa Na  Tinubu------Jibrin 

Gwamna 14 Ke Goyon Bayan Takarar Shugaban Kasa Na  Tinubu------Jibrin 

Akalla akwai gwamna 14 da dukkansu  kansu ke goyon bayan takarar shugaban kasa ta jagoran jam'iyar APC Asiwaju Bola Ahmad Tinubu a 2023.

Tsohon dan majalisar tarayya Abdulmumini Jibrin ne ya sanar da hakan ya ce akwai wasu karin gwamnoni hudu da aka fara magana da su domin marawa tafiyar baya.

Jibrin wanda yake babban darakta a majalisar kungiyoyin magoya bayan Tinubu haka ma ya ce shugabannin jam'iyar APC a jihohi 26 a fadin Nijeriya sun tabbatar da goyon bayansu ga tsohon gwamnan Lagos.
A turakarsa ta manhajar tweeter ya bayyana ya ce "Ba mu hanawa kowa fitowa takara mu dai muna goyon bayan Tinubu, kofofinmu a bude suke har bayan samun nasarar mu.