Gwamanatin Najeriya ta sanya Matatar Man Fatakwal Kasuwa

Gwamanatin Najeriya ta sanya Matatar Man Fatakwal Kasuwa
 
Daga Abbakar Aleeyu Anache 
 
Kamfanin mai na Najeriya NNPC ya tallata matatar mai ta garin Fatakwal da ta fara aiki ga ‘yan kasuwa masu zaman kansu wadanda zasu tafiyar da ita yadda ya dace.
 
Dama dai gwamnatin ta ce matatar zata fara aiki gadan-gadan cikin watanni hudun farkon wannan shekara, inda ake sa ran farawa  da tace ganga dubu 60 a kowacce rana kafin daga bisani a fara tace ganga dubu 210 kowacce rana.
 
Kamfanin ta cikin wata wasika da ya rabawa manema labarai, ya ce akwai bukatar baiwa ‘yan kasuwa masu sha’awa damar gwada basirar su wajen tafiyar da matatar don tabbatar da zamanta da kafafuwan ta ba tare da samun wata matsala ba.
 
Ana dai ganin nuna halin ko in kula na gwamnatocin baya ne ya kashe manyan matatun biyu da kasar ke da su, yayin da siyasa ta dabaibaye gyaran su, duk da alkawarin yin hakan da kowacce gwamnati ke yi a lokutan yakin neman zabe.
 
Sai dai kuma kamfanin ya ce duk dan kasuwar da ke bukatar karbar wannan matata sai ya nuna shaidar samun ribar akalla dala biliyan biyu tun daga shekarar 2019 a matsayin shaidar cewa shi dan kasuwa ne cikakke.
 
Ranar hudu ga watan da muke ciki ne aka gama duk wasu gwaje-gwaje a matarar abinda ke nufin a yanzu fara aiki ne kawai ya rage.