Gurɓataccen Abinci Da Aka Haɗa da Garin Masara ya kashe Karnuka 400
Ministan kiwon lafiya na kasar Zambiya, Elijah Muchima, ya nuna damuwarsa game da tsaron lafiyar ƴan kasar, bayan da karnuka 400 suka mutu sakamakon cin abincin da aka haɗa da masara.
Elijah ya ce bincike da gwajin da hukumomin ƙasar suka yi kan masarar ya nuna cewa kusan rabin samfura 25 da aka ɗauka daga kamfanonin haɗa abinci daban-daban na ɗauke da sinadarin aflatoxin mai guba, wanda ƙwayoyin cuta masu guba na 'fungi' ke samarwa.
Saboda haka ana zargin karnukan sun mutu ne bayan cin abincin da aka haɗa da gurbataccen masara.
Masara dai na ɗaya daga cikin abincin da aka fi amfani da shi a Zambiya, kuma gurbacewarta na haifar da babbar illa ga lafiyar ɗan'adam.
Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta yi gargaɗin cewa sinadarin aflatoxin na iya haifar da cutar sankarar hanta ga ɗan'adam..
Sai dai ma'akatar lafiyar ba ta bayar da rahoton mutuwar wani ɗan'adam ba sanadiyyar gurɓatatcciyar masarar.
Sai dai majiyoyi a cibiyar kula da lafiyar jama'a ta Zambiya sun ce a halin yanzu suna ƙokarin tantance ko gurɓataccen hatsin ya yi tasiri ga jama'a.