Gombe 2021 --DJAI ta tallafawa Mata 100 dan bunkasa sana'oin su
A kokarin Kungiyar nan ta taimakon al'umma musamman marasa gata ta Dangin Juna Afirka Initiative DJAI, ta tallafawa mata da jari a Gombe dan su samu hanyar dogaro da kan su.
Gombe 2021 --DJAI ta tallafawa Mata 100 dan bunkasa sana'oin su.
Daga Habu Rabeel, Gombe
A kokarin Kungiyar nan ta taimakon al'umma musamman marasa gata ta Dangin Juna Afirka Initiative DJAI, ta tallafawa mata da jari a Gombe dan su samu hanyar dogaro da kan su.

Kungiyar wacce take taron ta shekara shekara dan bada tallafi a wannan karon ta kashe fiye da naira dubu dari biyar wajen taimakawa Mata marsa karfi a garin Deba dake jihar Gombe Dan share musu hawaye.
Taron karo na 6 ya gudana ne a garin Deba fadar helkwatar Yamaltu Deba a jihar Gombe inda ya samu halartar mutane daban daban daga jihohi daban daban musamman Mambobin Kungiyar.
A jawabin sa na maraba da baki a gun taron shugaban Kungiyar Bashir Sani Dogo Katsina. Cewa ya yi taron shekara shekara suke yi a lokacin da suke ware Wani abu na musamman daga abun da suka tara dan tallafawa mabukata.
Bashir Sani Dogo, yace wannan Kungiya ta Dangin Juna Kungiya ce da ba ta gwamnati ba Kuma ba ta siyasa ba haka Kuma bata da alaka da addini.
A nasa tsokaci shugaban karamar hukumar Yamaltu Deba Hon. Shu'aibu Umar Galadima, Walin Deba, jinjinawa Kungiyar ta Dangin juna ya yi bisa wannan aikin alheri da suka yi daga cikin asusun kungiya na kudaden da suka tara.
Shu'aibu Galadima, ya Kuma ce hakan ya nuna cewa da ana samun kungiyoyi irin wannan suna tallafawa da an ragewa gwamnati dawainiya domin al'umma za su samu abun yi su dogara da kansu ba sai sun jira gwamnati ba.
Shi ma Mai Martaba Sarkin Deba Alhaji Ahmed Usman, cewa ya yi dangin juna sun cancanci a yaba musu domin sun taka rawar gani da za'ayi koyi da su.
" Da jama'a za su yi amfani da sunan wanann Kungiya Dangin Juna a zama Dangin Junan da ba za'a dinga samun tashe-tashen hankula a duniya ba balle ma ace za'a dauki dabi'ar taimakon na kasa".
Jigo a Kwamitin amintattu na kungiyar Alhaji Bashir Yahaya Bici, jan hankalin masu hanu da shuni ya yi da cewa su dinga tausayawa na kasa da su a kullum domin sama musu hanyar rayuwa da sauki.
Bashir Bici, ya kuma yabawa Mambobin kungiyar na yadda suke hada Kai wajen samar da tallafin da ake bai wa mabukata domin kudaden aljihun su suke cirewa su bayar Dan tausayin na kasa dasu.
A nata tsokacin Daraktar walwala da jin dadi na Kungiyar Hajiya Maryam Musthapha Maina Kiran matan da suka samu tallafin tayi da cewa su ririta dan abunda suka samu dan ya inganta su samu madogara
Maryam Maina, tace idan suka ririta kudin ta hanyar yin Sana'a nan gaba sune masu tallafawa wasu.
Daya daga cikin wadanda suka ci gajiyar Zurfa'au Muhammad da tayi magana a madadin sauran godewa Kungiyar tayi bisa abun alkhairi da suka kawo musu ba tare da sun roka ba.
Zurfa'au, tace wannan tallafin zai yi matukar bunkasa musu Sana'oin su wadanda basu da Sana'a Kuma sun samu hanyar farawa.
A baya Kungiyar ta gudanar da tarurrukan a garuruwa, Kano da Kaduna da Katsina da Naija da Bauchi yanzu Kuma a jihar Gombe
A karshen taron kungiyar ta karrama fitattun mutane a jihar da suke da babi'ar taimakawa mabukata.
managarciya