Gobara Ta Tashi a Ofishin Hukumar Zabe a Sakkwato

Gobara Ta Tashi a Ofishin Hukumar Zabe a Sakkwato

 

An samu tashin wata gobara a ofishin hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) da ke jihar Sokoto. 

Gobarar ta tashi ne a ofishin hukumar INEC da ke ƙaramar hukumar Gwadabawa, a jihar Sokoto. 
Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da kwamishinan INEC na ƙasa, Sam Olumekun, ya fitar a shafin X na hukumar.
Gobarar ta lalata aƙalla akwatunan zaɓe 558 da sauran kayayyakin zaɓe. 
Sam Olumekun ya bayyana cewa gobarar na iya kasancewa sakamakon wutar lantarki mai ƙarfi da aka kawo a yankin. "Gobarar ta tashi da sassafe a ranar Talata, 11 ga watan Fabrairu, 2025, inda ta yi mummunar ɓarna ga dukkan ginin ofishin." 
“Kayayyakin da gobarar ta lalata sun haɗa da kujeru da tebura, da kuma kayan zaɓe ciki har da akwatunan zaɓe 558, wuraren kaɗa ƙuri'a 186, jakunkunan zaɓe 186." 
"Sauran sun haɗa da tankunan ruwa 12 (masu cin lita 1,000), katifu 400 da botikai 300." 
"Jami'an tsaro da hukumomin kiyaye gobara da suka tura jami'ansu zuwa ofishin na ci gaba da binciken musabbabin tashin gobarar." 
"Ba a samu raunuka ko asarar rai ba a yayin tashin gobarar." - Sam Olumekun 
Ya bayyana cewa gobarar ta yi ɓarna sosai ga ofishin, lamarin da zai iya tasiri a shirye-shiryen zaɓe a yankin.
Hukumar INEC ta bayyana cewa tana ƙoƙarin duba yiwuwar maye gurbin kayayyakin da suka lalace domin tabbatar da cewa shirye-shiryen gudanar da zaɓe ba su samu cikas ba.