Gobara ta tashi a Jami'ar Sakkwato

Gobara ta tashi a Jami'ar Sakkwato
 

Mummunar gobara ta tashi a sabon ɗakin kwanan dalibai mata a jami’ar jihar Sokoto (SSU), lamarin da ya jefa al’umma cikin firgici. 

Wannan mummunan lamari ya faru ne da misalin ƙarfe 3:30 na yammacin ranar Talata, 25 ga watan Maris, inda gobarar ta babbake sabon ginin. 
Rahoton Legit.ng ya nuna cewa ɗakin kwanan da gobarar ta shafa yana cikin sababbin gine-gine da aka gina domin magance matsalar wurin kwanan dalibai a jami’ar. 
Har yanzu ba a gano musabbabin tashin gobarar ba, kamar yadda wata daliba ta shaidawa Legit.ng cewa "har yanzu ba a san abin da ya jawo tashin wutar ba." 
Dalibar ta bayyana cewa babu wani dalibi da ke zaune a cikin ɗakin kwanan a lokacin da gobarar ta tashi, saboda wani umarni da jami’ar ta bayar. 
A cewar dalibar da ta zanta da wakilinmu: "An riga an sallami daliban da ke zaune a wannan sabon ɗakin kwanan, inda aka mayar da su tsohon ɗakin kwana. 
Mahukuntan makarantar ne kawai suka san dalilin daukar matakin." 
Shugaban ɗalibai a jami’ar ya tabbatar da cewa jami’an kashe gobara sun isa wurin da misalin ƙarfe 5:00 na yamma domin dakile wutar.